Wani mutum ya ɗan ƙasar Vietnam ya janyo cece-kuce bayan yayi iƙirarin cewa ya shafe shekaru da dama bai ko runtsa ba.
Bidiyon mutumin ya karaɗe shafukan sada zumunta, inda yayi iƙirarin cewa rabon shi da barci tun shekarar 1962. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
Mutumin mai suna Thai Ngoc ya bayyana cewa tsawon shekara 65 bai ko runtsa ba domin samun barci.
KU KARANTA KUMA: Ba namijin da zai mayar da hankalinsa kacokan kan mace -Wani ɗan kasuwa
Wani mai sanya bidiyoyi a Youtube, mai suna Drew Binsky, shine ya bi Thai Ngoc har ƙasar su domin haɗuwa da shi. Ya dai sanya bidiyon Thai ne a manhajar Insragram.
A cikin bidiyon, an nuna mutumin yana zuƙar sigari sanann idanun sa a buɗe lokacin da yake a kwance.
Sai dai mutane da yawa a Instagram sun bayyana cewa da ace ya kwashe wannan tsawon lokacin ba tare da barci da tuni ya kwanta dama.
Wasu kuna sun bayyana cewa jikin ɗan adam ba zai iya jure wannan tsawon lokacin ba, ba tare da samun barci ba.
A cewar wata kafa ta Healthline, wacce ke bayar da bayanai kan lafiya, mutum ka iya fara zaucewa idan ya ɗauki dogon lokaci bai yi barci ba.
Bayanin da suka yi na cewa:
“Lokaci mafi tsawo da aka taɓa samu ba tare da barci ba shine sa’o’i 264, ko kwana 11 a jere. Duk da dai har yanzu ba a san iya tsawon lokacin da ƴan adam za su iya ɗauka ba tare da barci ba, bai ɗaukar wani dogon lokaci illolin rashin samun barci ke fara bayyana.”
Sauya Fasalin Kudi, Ya Kawo Saukin Garkuwa, Da Aiyukan Ta’addanci — Emefiele
A wani labarin na daban kuma gwamnan babban bankin Najeriya ya bayyana sauyin da sababbin kuɗi suka kawo.
A ranar Talata Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, ya yi kira ga ‘yan majalisar dokoki da ‘yan Nijeriya da su fahimci alfanun dake cikin sauya fasalin kudi, yana mai jaddada cewa babban bankin na shirin yaki da matsalar rashin tsaro a Najeriya.
Emefiele ya kuma yi ikirarin cewa lamarin sace-sacen mutane da fashi da makami ya ragu yayin da aka sake fasalin kudin Naira.