Dalilan da suka sanya APC zata faɗi zaɓen Gwamnan Ekiti — Inji PDP
Babbar Jam’iyyar Hamayya ta PDP tace Jam’iyyar APC zata faɗi zaɓen 18 ga watan yuni na Gwamna a Ekiti.
Ƙungiyar gangamin yaƙin neman-BKCO Bisi Kolawole ta lissafo rashin biyan haƙƙoƙin ma’aikata, a lalacewar gine-gine da Matsalar Tsaro a matsayin dalilai.
Ɗan takarar APC Biodun Oyebanji ya taɓa cewa irin namijin ƙoƙarin Gwamna Kayode Fayemi zai taimakawa Jam’iyyar ta samu nasarar zaɓe.
KARANTA WANNAN LABARIN: Jahar Delta ta rufe Makarantar da Ɗalibi mai watanni 19 ya mutu, bayan Dukan Malami
Jam’iyyar PDP tace Oyebanji zai fara da kawo tsaro daya maida hanyoyin Ekiti wani abu daban na garkuwa da mutane, da korar ma’aikata, da lalatattun hanyoyi da satar kuɗaɗen jama’a.
Wannan sanarwar na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai Magana da Yawun Ƙungiyar BKCO Lere Olayinka, inda ya nuna damuwa na yadda Malamai suka bada gudunmawar Naira 500 domin amso ɗan uwan su.
Comments 1