Dalilan da suka sanya Ministoci, Masu Muƙami ke ruguguwar Kare Buhari — Femi Adesina
Mai Baiwa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari na musamman akan Kafafen Yaɗa Labaru Femi Adesina ya bayyana dalilan da suka sanya wasu Ministocin da sauran masu muƙamai a kowane lokaci suke kare Shugaban Ƙasa a ciki ko wajen ofishin su.
KARANTA WANNAN LABARIN: FG ta fara yunƙurin shawo kan yajin aikin ASUU, ASUP, ta fara biyan kuɗaɗen Ariyas
Yace mutunta dukkanin masu muƙamai da sauran waɗanda suke aiki tare dashi, na daga cikin dalilan da suka sanya wanda ke tattare dashi suke rige-rigen kare shi.
Adesina ya bayyana haka a cikin wani jawabi daya fitar akan abinda ta shafi muƙarraban Buhari, da aka tura a Kafar Sadarwa ta Facebook a ranar Alhamis.
Hadimin yace mutunta Ɗan Adam na Buhari ya sanya yayi bikin bankwana da dukkanin muƙarraban shi da suka ajiye aiki, domin yin takara a muƙamai daban-daban.
A cewar sa ko a Shekarar 2015 Buhari ya gaji Hafsoshin Tsaro, amma ya cigaba da tafiya dasu ba tsawon watanni biyu, kuma ranar daya canja su, ya turo man sunayen waɗanda yake so su gaje su.
“Bayan turo da sunan Buhari ya bada umarni, yace na tattauna da Hafsoshin Tsaro, amma kada kayi saurin sanar da korar su. Bari sai sunje gida, sannan su zama wanda zasu sanar da iyalan su da Abokanan su. Babu daɗi mutum ya zamanto yana da aiki da safe da yamma ya rasa kuma sai dai yaji hakan a Kafafen Yaɗa Labaru.”
Comments 1