Jarumi Shahid Kapoor yana daga cikin jaruman India da suke kan bayar da gudun mawa a masana’antar shirya fina-finai ta ƙasar India wato Bollywood, kuma masana’anta ce wadda ita kanta gwamnatin ƙasar take samun kuɗaɗen shiga duba da yadda fina-finan Indiya suke samun karɓuwa a duniya.
Tun kafin shigowar cutar nan data addabi duniya wato Coronavirus akwai kamfanin da yayi niyyar yin fim maisuna Jersey inda kamfanin ya bayyana cewar Shahid Kapoor ne zai taka rawar gani a cikin fim ɗin kuma a lokacin jami’an kamfanin suka yarda cewar zasu yi wannan fim, sai dai shi Shahid Kapoor ya kafamusu sharaɗin cewar sai an bashi kimanin adadin kuɗaɗen da suka kai karo 33 a wancan lokacin sannan zai sanya hannu yayi wancan aiki na fim.
Sai dai kuma suna tsaka da shooting ɗin film ɗin sai annobar Coronavirus ta bayyana inda hakan ya sanya aka dakatar da yin shirin film ɗin, biyo bayan cewar a ‘yan kwanakinnan aka bayyana cewar za a buɗe sinimun ƙasar Indiya hakan ta sanya duk wani fim da ba’a kammala ba aka fara dawowa domin ci gaba da yinsa.
Haka zalika bayan hakan masu jagorantar shirya film ɗin a halin yanzu sun sake yin zama da jarumi Shahid Kapoor akan maganar manyan kuɗaɗen da yace za a bashi tun farko inda suka nunamasa cewar ya kamata ya rage farashi duba da yadda tattalin arziki take tangal-tangal a duniya sabo da cutar Covid 19, inda yanzu ya nemi da a biyashi Karo 25 (Crore) maimakon 33 da sukayi yarjejeniya kafin a fara annobar cutar nan data addabi duniya wato Coronavirus.
Wannan fim maisuna Jersey fim ne da Gautan Tinnanuri yake bayar da umarni sannan kum Allu Aravind da Aman Gill da kuma Dil Raju suka shirya, jaruman cikin wannan fim sun haɗar da Shahid Kapoor wanda ya fito a maisuna Arjun Raichand, sauran jaruman sune Pankaj Kapur da kuma jaruma Mrunal Thakur. Fim ne da aka yishi a ƙasar India kuma anyi amfani da yaren Hindi.
Shidai wannan fim an fara yin shirunsa tun a watan Oktoba na shekarar data gabata ta 2019 kuma anso a sakeshi a watan Ogusta na shekarar da ake ciki ta 2020 amma sabo da annobar cutar Coronavirus hakan bai yiwwuba inda sai a yanzu ma za aci gaba da yin wannan fim.
Labarin fim ɗin a taƙaice shine Shahid Kapoor ya kasance yana fafata wasan Cricket kuma ya iya sosai a matsayinsa na ɗan shekara 36 amma kuma kwatsam sai ya dena fafata wasan harna tsawon shekaru 10, bayan hakan ta faru kuma shine ya dawo ci gaba da wasan inda zai wakilci ƙasarsa ta India a matsayinsa na shahararren ɗan wasan Cricket kuma yana da shekaru 46 kenan.
Sai dai idan ba’a manta ba a yankin Telegu na ƙasar ta India anyi film mai irin wannan sunan wato Jersey kuma an sakeshi a shekarar data gabata ta 2019, sai da labarin wancan fim ɗin da wannan na yanzu kwata-kwata sun bambanta sosai da sosai inda kowanne da irin yaren da akayishi daban.
Sai dai Shahid Kapoor ya bayar da tabbacin cewar da zarar an saki wannan shahararren fim da ya jagoranta to babu makawa zai kawo manyan kuɗaɗe kuma zaiyi wuta sosai a kasuanni, sannan Shahid ya ƙara da cewa kamar yadda wasu manyan fina-finai suka ajiye tarihi a masana’antar ta shirya fina-finai ta Indiya shima wannan fim zai iya shiga sahunsu.