Hukumar ƙwallon hannu ta ƙasar nan ta bayyana cewar a halin yanzu babu wani shirye-shirye data keyi face shirin tunkarar fafata wasannin guje-guje da tsalle-tsalle wato Olympics daza a yi a birnin Tokyo na ƙasar Japan a sabuwar shekara mai kamawa ta 2021, kuma a gasar ta Olympics ana fafata wasanni da dama kusan babu irin wasan da ba’a fafata shi.
Wannan magana ta fito ta bakin shugaban hukumar wato Eng. Musa Nimrod yayin wata tattaunawa da akayi dashi da Radiyo Najeriya dake babban birnin Bayelsa wato Yenagoa inda a lokacinne yake baygana hakan. Sannan ya ƙara da cewar burinsa a ƙarƙashin jagorancinsa yaga anyi nasarar da ba’a taɓa yiba musamman a gasar ta guje-guje da tsalle-tsalle.
Haka zalika ya sake cewa ‘yan wasan na ƙwallon hannu ɓangaren maza dana mata dukkaninsu a shirye suke domin tunkarar wasannin na gasar ta Olympic duk da cewar har yanzu suna kan ƙadamin fafata wasannin share fage na gasar musamman ɓangaren maza duba da cewar ko wanne ɓangare akwai matasan ‘yan wasa dazasu kai Najeriya ga gaci.
“Duk wannan ƙoƙari da mukeyi akan ‘yan wasannan maza da mata baya rasa nasaba da kada mu maimaita kurakuren da mukayi a gasar guje-guje da tsalle-tsalle a birnin Rio de Janeiro na ƙasar Brazil fake yankin kudancin Amurka, inda a waccan gasa abubuwa marasa daɗi sun faru kuma masu ɗaci sosai da sosai”
Gasar ta guje-guje da tsalle-tsalle anso a gudanar da ita a wannan shekarar ta 2020 amma kuma sabo da annibar cutar nan ta Coronavirus ta sanya ba a sami damar gudanar da gasar ba shine aka bayyana cewar sai a shekara mai kamawa ta 2021 za a fafata gasar a birnin na Tokyo dake yankin Asia na ƙasar Japan.
Daga ƙarshe Musa Nimrod ya bayyana cewar irin ƙoƙarin da ‘yan wasan na ƙwallon hannu sukayi a wasannin Afrika da aka kammala a ƙasar Morocco da kuma wasaninin da sukayi a birnin Humberg na ƙasar Jamus a shekarar data gabata irin gudun mawar da sukayi da kuma rawar ganin da suka taka shine ya nuna cewar babu makawa zasuyi abin azo a gani a gasar ta guje-guje da tsalle-tsalle a shekarar 2021 mai kamawa a birnin Tokyo na ƙasar Japan.