An harbe wani mawaki dan kasar Amurka, Rakim Hasheem Allen, AKA PnB Rock har lahira.
Daily Post ta ruwaito cewa, An harbe PnB Rock a wani fashi da makami da aka yi a Kudancin Los Angeles na Amurka a daren jiya Litinin.
KARANTA WANNAN LABARIN: Masarautar Kano Zata Daura Damar Neman Al’umma Su Mallaki Katin Dan Kasa
Kafar yada labarai ta Los Angeles Times ta ruwaito cewa an harbe shi ne a lokacin da ake yin fashi a gidan Roscoes’s House of Chicken & Waffles bayan budurwarsa ta wallafa wani hoto a Instagram tare da alamta wuri da take.
Da yake magana kan lamarin, Babban jami’in Dan sandan dale kula da yankin Los Angeles, Kelly Muniz, ya ce wani da ake zargi dauke da makami ne ya shiga gidan cin abincin ya bukaci kayan adon dake jikin Rock.
Ya kara da cewa, “Ya harbe mawakim sannan ya fita da gudu ta kofar gefe zuwa motar da za ta tafi, sannan ya gudu daga wurin ajiye motoci,” in ji shi
A WANI LABARIN KUMA: Yan sanda Sun Yi Martani Kan Tarwatsewar Wani Abun A Jigawa
Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta ce fashewar iskar gas da ta afku a karamar hukumar Babura ta jihar ta raunata mutane bakwai tare da lalata shaguna 17 da gidaje biyar.kamar yadda DAILY POST ta ruwaito
Dimokuradiyya ta rawaito cewa fashewar iskar gas ta raunata mutane tare da lalata gidaje da shaguna a Babura a daren jiya Litinin.