Wasu ma’aikatan ma’aikatar kudi ta jihar Bauchi, Nasiru Samaila da Auwal Jibrin, sun hada baki da wasu mutane biyu wajen zambar kudi naira 332,000 ga abokin aikinsu, Jibrin Adamu wanda ya rasu a watan Disambar bara.
Sun samu nasarar wannan kwamachalar ne da taimakon wani ma’aikacin gidan yanar gizo, Tijjani Mohammad da Faruq Mohammad Nasiru, dalibin Abubakar Tatari Polytechnic (ATAP) da ke ma’aikatar don samu hora na musamman.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi, Ahmed Wakil, a wata sanarwa da ya fitar, ya bayyana cewa wadanda ake zargin sun yi mallaki takardun bogi ne na marigayin, wanda mazaunin kauyen Zalanga ne a karamar hukumar Ganjuwa.
KARANTA ANAN: Masarautar Kano Zata Daura Damarar Neman Al’umma Su Mallaki Katin Dan Kasa
Wakil ya bayyana cewa Samaila mai shekaru 48 ya yi amfani da kwarewarsa na tsawon shekaru 17 a ma’aikatar inda ya kitsa badakalar da ya ciro Naira 212,000 daga cikin kudin, yayi da babban abokin aikin sa Jibril ya samu N100,000.
Mohammed, ma’aikacin gidan yanar gizo, wanda ya taka rawar bada tabbacin Mohammed, wanda ya yi kama da wani cikin dangin marigayin, tare da samun N20,000.
A wani bangare sanarwar ta kara da cewa, “Bincike na farko wanda ya nuna cewa; wani Nasiru Samaila mai shekaru 48 a duniya ma’aikacin ma’aikatar kudi ta jihar Bauchi, ya hada baki da wasu mutane uku da suka hada da; Auwal Jibrin mai shekara 27 a ma’aikatar kudi Tijjani Mohammad mai shekaru 27 a jihar Bauchi mai karancin kudi, Faruq Mohammad Nasiru mai shekara 19 dalibin Kwalejin Fasaha ta Abubakar Tatari ta hanyar son kai da rashin tausayi kuma sun samu kudaden da suka kai naira dubu dari uku da talatin da biyu (N332,000) na mamacin suka mayar da su zuwa ga amfanin kansu, sun raba riba a tsakaninsu.”
Shirin holen su din yazo ne bayan da wata i
makudanciyar marigayin Samira Jibrin, ta kai karar ga ‘yan sanda, tare da neman a gaggata daukar mataki.
Wakil ya ci gaba da cewa mutanen hudun sun amsa laifin da suka aikata, inda ya kara da cewa kwamishinan ‘yan sandan jihar (CP) Umar Sanda, ya bayar da umarnin a gurfanar da su a gaban kotu.
A wani labarin kuma: Dan bindiga Ya Harbe Wani Shahararren Mawakin Amurika Har Lahira
An harbe wani mawaki dan kasar Amurka, Rakim Hasheem Allen, AKA PnB Rock har lahira.
Daily Post ta ruwaito cewa, An harbe PnB Rock a wani fashi da makami da aka yi a Kudancin Los Angeles na Amurka a daren jiya Litinin.