Wani mutum ya kai wa mai goge-goge farmaki yayin da ya kama shi yana lalata da wata mace a bayi, LIB ta ruwaito.
Mutumin mai suna Billy Dean Fallon, mai shekaru 28 yana tsaka da lalata da wata mata sai mai goge-goge ya fara kwankwasa kofar bayin, nan da nan ya fito ya fara dukan mai goge-gogen.
Yayin da aka gurfanar da shi a gaban kotu, a ranar Litinin, 7 ga watan Oktoba, ya amsa laifinsa. Hakan yasa aka umarce shi da biyan mai goge-gogen $1,500.
Lamarin ya auku ne a wani gidan rawar dare da ke Burleigh Heads a Janairun wannan shekarar.
Kamarar CCTV da aka bayyana wa kotu ta nuna yadda mutumin ya fito daga bayin babu ko riga inda ya hau nushin mai goge-gogen yana buga shi da kofa har na tsawon mintoci uku.
An ga wata mata tsaye a wurin rike da lemu guda biyu tana kallon Fallon yayin da yake dukan mai goge-gogen.
Daga bisani jami’in tsaro ya kwace mai goge-gogen kafin ya sanar da ‘yan sanda halin da ake ciki.
KU KARANTA: Bayan satar awakai biyu, wani matashi ya samu tikitin zaman gidan yari
A ranar Talatar nan ne wata kotu a yankin da ke garin Jos ta yanke wa wani matashi, Pius John, mai shekaru 20 da haihuwa, hukuncin zaman gidan yari na watanni tara.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Kotun ta yanke masa wannan hukuncin ne bisa samunsa da laifin satar awaki biyu.
Wani kwamitin alkalai guda biyu, Adam Sadiq da Hyacinth Dolnaan da suka yanke wa John hukunci, sun ba shi zabin tarar Naira 10,000.
An kuma umarci mai laifin da ya biya diyyar N40,000 ga wanda su kai karar sa.
Sun ce hukuncin zai zama katanga ga masu son aikata irin wannan aika aika.