Daga Sulaiman Musa
Wani dan kasuwa mai suna Dakta Andrew Warri Foubiri, ya nemi diyyar naira biliyan biyar tare da neman afuwa daga wajen hukumar EFCC bisa abun da ya yi zargi na fata suna da kuma ayyana nemansa ruwa a jallo da hukumar ta yi ba tare da bin matakan da shari’a ta gindaya ba.
Fuobiri wanda shine Manajan Darakta na kamfanin A.M Project Consultancy Limited, MD Ranez Medicalas ya yi wannan bukatar ne ta hannun lauyansa Cif Nelson O. Imoh da Kini Inemkpo Marcus a wani wasika mai kwanan wata 14 ga Afrilun 2021.
EFCC dai ta wallafa a jaridun da ke fita kullum tana nema Fuobiri ruwa a jallo bisa zargin badakalar miliyan 125.
EFCC dai ta yi ikirarin cewa ta bi matakan shari’a wajen yin hakan domin ta je kotu domin neman wanda take nema.
A martanin Fuobiri ya bayyana cewar EFCC ta yi rigamalam masallaci ne kawai, domin kuwa kotu ce ke da alhakin sauraron wannan shari’ar tun da na gabanta.
Ya ce, tallar da EFCC ta yi, kawai domin bata masa suna ne, don haka ne yake neman diyyar biliyan biyar da kuma afuwa daga hukumar.