Daga Sulaiman Musa
Wasu ‘yan bindiga dadi da safiyar yau ne suka kai hari gidan gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma, inda suka banka wa gidan wuta tare da kona motocin da suke ajiye a cikin gidan gami da kashe jami’an tsaro biyu.
Gidan gwamnan da ke Omuma, a Gabashin Karamar hukumar Oru, a jihar Imo.
Masu kai harin sun yi hakan ne kwana guda bayan da gwamna Uzodinma ya gaba da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadarsa da ke Abuja inda ya roki shugaban karin jami’an tsaro a jihar.