A sanyin safiyar yau Talata ne aka hallaka wani jami’in dan sanda yayin da yake kokarin ceto wasu mutane da ake shirin Garkuwa da su a Tungan Maje dake unguwar Gwagwalada na birnin tarayya Abuja.
Wani mazaunin unguwar da aka bayyana da Ibrahim Saidu ya ce yan bindigar sun yi ta musayar wuta tsakaninsu da yan sanda da ma yan Bijilanti gabannin hallaka dan sandar.
Ya ce yan bindigar sun fara kai farmaki ne a wani lungu mai suna Anguwar Samu duk dai a Tungan Maje inda suka yi awun gaba da mutane biyu bayan musayar wuta ta kusan awa guda da jami’an tsaron.
A cewar shi bayan da yan bindigar suka ga jami’an tsaron sun yi galaba a kan su nan da nan suka sauya dabara inda suka nufi wata unguwa ta New Poultry Area inda nan ma suka arce da karin wasu mutane biyu.
Bugu da kari ya ce jami’in dan sanda da kuma dan Bijilanti da suka jikkata tuni an garzaya da su wani asibiti da ba a bayyana.
Kawo yanzu dai Kakakin Rundunar Yan Sandan birnin tarayya Abuja Maryam Yusuf ba ta ce kala ba dangane da lamarin dul da irin kiraye-kiraye da kuma sakon kar-ta-kwana da aka aike mata.