Dan takarar gwamnan Kano na jam’iyyar NNPP Abba Kabir Yusuf, ya shirya kaddamar da manufofin da take fatan cimma idan ya samu nasara, tare da kwamitin yakin neman zaben sa a zaben 2023 .
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa mai magana da yawun Dan takarar Sanusi Bature Dawakin Tofa ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar mai dauke da sa hannu.
KU KARANTA: Yadda Rikicin Kudin Kanana Hukumomi Ta Faro Tsakanin Su Da Gwamnoni – Atiku
Cikin sanarwar Abba Gida Gida zai gabatarwa da al’ummar Kano abokin takararsa Aminu Abdussalam Gwarzo.
Ana saran bikin zai gudana a ranar Talata 6 ga Disambar 2022 a dakin taro na Meena da ke jihar Kano.
Kuma ana sa ran bikin zai samu halartar shuwagabannin jam’iyyar, ‘yan kasuwa, malaman addini da kungiyoyin fararan hula daban-daban.
Abin jira a gani shine irin abubuwan da suka kasance cikin manufofin sa na mulkin, idan yayi nasara.
A wani labarin kuma: Ka Rage Kudin Jami’ar Ka Ga Ya’yan Talakawa Idan Kana Kishin Ilimi – Kwankwaso Ya Caccaki Atiku
Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya kamata ya rage kudin makaranta a jami’ar sa ta Amurka dake Najeriya, idan har ya rike ilimi da gaske a kasar nan,” inji Rabiu Kwankwaso.
Kwankwaso, wanda tsohon gwamnan Kano ne kuma dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP, ya bayyana a zauren taron na daren yau cewa Abubakar zai tabbatar da cewa ya dauki lamarin Ilimi da muhimmanci idan ya rage kudin makarantar.