Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya yi karin haske kan rikicin da ya barke a cikin kudaden da gwamnatin tarayya ke fitarwa da kuma yadda ake sarrafa irin wadannan kudade tsakanin jihohi da kananan hukumominsu.
Atiku ya ce matsalar ta faro ne a lokacin da yake rike da mukamin mataimakin shugaban kasa, inda ya ce shi ne ya jagoranci kananan hukumomi inda ya tabbatar da cewa an tura kudaden kananan hukumomi kai tsaye zuwa asusun kananan hukumomi.
KU KARANTA: Rayuwata Na Cikin Hatsari Saboda Fallasa Karerayin Dake Cikin Takardun Gwamna Mai Ci, Jigon PDP
Atiku wanda ya yi magana a cikin jerin shirye-shirye na 3 na yan takarar shugaban kasa da ke gudana, wanda gidan Talabijin na Arise ta shirya a ranar Lahadin nan.
Ya bayyana cewa manufofin da ya aiwatar sun nuna rashin amincewar su da gwamnonin lokacin da suka lura ba bisa ka’ida ba ne.
Atiku ya ce ya zama wajibi a duba kundin tsarin mulkin kasar domin ganin yadda kananan hukumomi za su samu ‘yancin cin gashin kansu ta fuskar kudaden shiga da kudadensu.
A wani labarin kuma: Yan Sandan Sudan Sun Saki Wani Mai Fafutukar Yaki Da Cin hanci Da Rashawa
An sako wani fitaccen dan siyasar Sudan daga gidan yari kwana guda gabanin kawancen farar hula da ya ke da shi ya rattaba hannu kan wata yarjejeniya ta farko da sojoji domin kawo karshen takaddamar siyasa da ya haifar da juyin mulkin watan Oktoban 2021.
Dan siyasar Wagdi Salih, wanda aka sake shi ranar Lahadi a ofishin ‘yan sanda a Khartoum babban birnin kasar, yana kan gaba a kwamitin yaki da cin hanci da rashawa da aka kafa bayan hambarar da tsohon shugaban Sudan Omar al-Bashir a shekara ta 2019.
Kwamitin da aka dorawa alhakin rusa gwamnatin Al-Bashir, ya fuskanci suka daga janar-janar da ke raba madafun iko da farar hula na ‘yanci da sauyi (FFC) kafin su gudanar da mulkinsu, tare da dakatar da mika mulki da ke da nufin kai ga zaben dimokuradiyya.