An bayyana dan takarar jam’iyyar APC mai mulki a yankin Gwagwalada Alhaji Abubakar Jibrin Giri a matsayin wanda ya lashe zaben gundumar da aka gudanar ranar Asabar a yankin.
Jami’in zabe na INEC a yankin, Farfesa Iliyasu Umar, wanda ya bayyana hakan a ofishin INEC a yau Lahadi, ya bayyana cewa dan takarar APC, Giri ya samu kuri’u 11, 125 inda ya doke dan takarar PDP, Mohammed Kasim Ikwa, wanda ya samu 9. 597 kuri’u.
Wakilin Jaridar Daily Trust ya ruwaito cewa jami’an tsaro sun killace ofishin hukumar na INEC yayin sanar da sakamakon zaben.
A wani labarin Kuma na daban.
Akalla mutane uku ne suka mutu tare da ceto wasu mutane biyu da ransu a karkashin baraguzan ginin bene mai hawa uku da ya ruguje a unguwar Yaba da ke jihar Legas ranar Asabar.
Rahotanni sun bayyana cewa ginin bene mai hawa uku da ake ci gaba da yi ya ruguje inda ya rufta kan wani ginin da ke gefensa a Akanbi Crescent a unguwar Yaba a jihar Legas.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Legas da wasu masu aikin ceton da suka isa wurin, an ce sun isa wurin ne sa’o’i guda bayan rugujewar domin fara aikin ceto.
Darakta Janar na LASEMA, Olufemi Oke-Osanyintolu, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce dukkan gawarwakin da aka gano manyan maza ne, kuma ana ci gaba da kokarin ceton rayuka.
Oke-Osanyintolu ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Nosa Okunbor, ya fitar mai take, ‘Rahoton Halin da ake ciki kan Rugujewar Gine-gine a Titin Akanbi Kusa da Babban Kofar Unilag’.
Ya bayyana cewa jami’an agajin gaggawar sun kwaso gawarwakin tare da ceto wasu da ke raye sakamakon tura manyan na’urorin hukumar cikin gaggawa.
Sanarwar ta kara da cewa, “An sabunta: An kuma gano wani babba namiji da ya mutu a karkashin baraguzan ginin.
“Jimlar ƙidaya har zuwa karfe 23:00 na safe. An ceto mutane 2 manya maza a raye inda aka samu Matattu 3 manya maza.”
Ya kara da cewa har yanzu ana ci gaba da aikin ceto ga sauran wadanda abin ya shafa.