Tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta AC Milan, Real Madrid, Ajax, Sampdoria da Inter Milan Clarence Seedorf ya karbi kalmar shahada ajiya Alhamis.
Tsohon dan wasan na kasar Netherlands wanda a baya cikakken sunan sa shine, Clarence Cycle Seedorf, Amma bayan ya koma addinin musulunci ajiya ya mayar da sunan sa ya koma Younis.
Seedorf yana daya daga cikin manyan ‘yan wasan kwallon kafa a tarihin kasar Netherlands, Bayan ya fafata wasanni sama da guda 300 ya jefa kwallaye 45 a AC Milan.
Akwai ‘yan wasan kwallon kafa da dama wadanda suka sauya addini zuwa addinin musulunci, Saidai wasu ‘yan wasan suna shirin dawowa amma saboda tsoron kyara da tsangwama daga wajen ‘yan uwan su basa iya aiwatar da hakan.