Gwamnatin jihar Delta ta ce ta samu jarirai 22 da aka haifa a sansanonin ‘yan gudun hijira da ke jihar.
Sakataren gwamnatin jihar kuma shugaban kwamitin kula da ambaliyar ruwa na ma’aikatun gwamnatin jihar Cif Patrick Ukah ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a Asaba.
KARANTA ANAN: Zamfara: CP Kolo Ya Ziyarci Wasu Makarantu Tare Da Tabbatar Da Inganta Tsaron Su
Ya ce asarar da jihar ta yi zai fi muni idan ba don jajircewar gwamnatin jihar ba.
Ukah ya yabawa kamfanoni masu zaman kansu dangane da bala’in ambaliyar ruwa, inda ya ba da tabbacin cewa nan ba da dadewa ba gwamnatin jihar za ta buga sunayen masu hannu da shuni a cikin wani cikakken shafi na talla a jaridu domin jihar ta yabawa kowannensu.
Kwamishinan ya kara da cewa, hasarar da aka yi da ambaliyar ba a iya tantancewa ba, inda ya ce har yanzu gwamnatin jihar ba ta samu wani kudi daga gwamnatin tarayya ba in ban da wasu kayan agaji da hukumar NEMA ta bayar.
A wani labarin kuma: Da Dumi-Dumi: Bata Gari Sun Bankawa Ofishin INEC Wuta A Ogun
Wasu da ake zargin bata gari ne sun kona ofishin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da ke Iyana, a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun.
DAILY POST ta ruwaito cewa ‘yan ta’addan sun kai kimanin takwas, sun haure katangar, inda suka shiga harabar kuma suka cinna wa ginin INEC wuta daga baya.