Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Legas, Bala Elkana a cikin wata sanarwa da ya fitar ya bayyana cewa; sun tsare mutane 58 bisa laifin kin saka takunkumin fuska.
Sannan sanarwar ta ce sun kuma kama wasu mutum 121 wadanda suka kin bin dokar hana fitan dare sannan an kama motoci 79 wadanda ba su bi umurnin dokar hana fita ba.
Sanarwar ta ce a jumlace an damke mutum 325 a ranar Litinin kuma duk an gurfanar da su a gaban kuliya inda daga karshe aka yanke musu hukunci.