Dole A kama Sheik Gumi, Inji Femi Kayode
Tsohon Ministan Jiragen Sama yace ya kamata a kama Babban Malamin Addini Sheik Gumi.
Ya bayyana hakane a shafinsa na Twitter kan irin kokarin kare masu garkuwa da Mutane da yakeyi a Arewa.
KARANTA:-Shugaban Sojojin Najeriya ya Ziyarci Shehun Borno
A ranar Juma’a data gabata ne Malamin ya karyata maganar da akeyi Hukumar Binciken Sirri sun gayyace shi.
Kamar yada Jaridar pmnews ta wallafa tace ” Malamin yasha kare Yan bindiga idan sun dauke Dalibai da matafiya da kuma wadanda suke zaune a gidansu.
Sukace yace Yan bindigan sunayi don su samu kudi badon su kashe Mutane ba.
A baya yace Sojoji da Yan sanda sukan hada kai da Yan Bindigan don cigaba da ta’addanci a Arewa.
Duba da irin wadannan zantuttukan tsohon Ministan yace tuni ya kamata a kamashi kamar yadda ya ayyana.
“Matsalar bashi ne zuwanka dajin ba sai dai abunda ka fada lokacin da kaje can, meyene kake samu da kake kokarin karesu da wankesu akan irin mummunan aikin da sukeyi.
Kai ne babban abokinsu, shiyasa ka zama dan bindiga Kuma tuni ya kamata a kama ka.
Sai dai Sheik Gumi yace duk abunda yakeyi gwamnati na sane hakama hukumar Yan sandama na sane.
Comments 1