Gwamnan Jahar Rivers Nyesom Wike a ranar Laraba, yace dole a miƙa mulki zuwa kudu indai ana son zaman lafiya ya ɗore a ƙasar.
Ya bayyana haka a lokacin da yake wata lekca, ga mahalarta taron masu karatun Sanin fasahohi da bayanan sirri na 14, a cibiyar horas da tsaro a Abuja a ranar Laraba.
Gwamnan yace “idan mutane suka ce tsarin karɓa-karɓa baya cikin kundin tsarin mulkin Nigeria, kasan mi ake nufi da adalci? Adalci shike kawo zaman lafiya. Kowa ya kamata ya zama ɓangare a ciki. Domin daga lokacin da ka fahimci cewa, kai baka ciki, sai faɗace-faɗace.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ka Ayyana ‘Yan Fashin Daji A Matsayin ‘Yan Ta’adda –Sakon Majalisa Ga Buhari
“Daga lokacin da ka fara hana mutane wasu abubuwa, wannan zai haifar da matsalar tsaro, domin bazaka iya cimma muradun ƙarni ba.
Wike ya cigaba da cewa, “misali ka ɗauki inyamurai da suke kuka akan naɗe-naɗe, miyye matsala don ka saurare su?
“Miyye matsalar don kazo kace duk ɗaya muke, kuma muna son wannan ƙasar ta zamanto a tare, domin cimma muradun ƙarni, domin idan baka sanya dasu ba, to wasu daga ciki zasu fara tunanin basa cikin gwamnati.
A cewar sa, babu wata jaha a Nigeria da take matsiya ciya domin kawai anyi dogaro ne kai tsaye da Gwamnatin tarayya, inda ya ƙara dacewa, Gwamnoni ya kamata su riƙa amfani da ɗimbin albarkatun ƙasa a Jahohin su.
“Duk jahar datace matsiya ciya ce to kawai tana ɓata maku lokaci da faɗar hakan. Ina jadadda cewa idan jahar ka matsiya ciya ce miyasa kake son zama Gwamna, kuma kake son a zabe ka har wa’adi na biyu.”