Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya nuna takaicinsa kan yadda tsaron kasar ke kara tabarbarewa.
Shugaban a ranar Talata ya ce an bai wa jami’an tsaro cikakken ‘yancin tunkarar matsalolin kashe-kashe a kasar, amma duk da haka kullum ci gaba da farmakar jama’a suke yi.
Buhari na mayar da martani ne kan jerin kashe-kashen da ‘yan ta’adda suka yi wa mazauna jihohin Sokoto, Kaduna da Filato.
Kamar yadda ya saba, Buhari ya jajantawa wadanda suka rasa ‘yan uwansu a hare-haren wuce gona da iri da aka kai a yankunan.
Shugaban wanda ya yi nazari kan lamarin bayan rahotannin asarar rayuka da dama a hare-haren, ya ba da tabbacin goyon bayan gwamnatin tarayya ga jihohin.
Ya kara da cewa “mun baiwa jami’an tsaro cikakken ‘yancin yin maganinsu, da kuma kawo karshen wannan hauka.”
“Na yi Allah-wadai da wadannan hare-haren wuce gona da iri kan kasar, kuma Ina so in tabbatar wa jihohi duk wani goyon baya daga gwamnatin tarayya.
“Tunanina yana tare da iyalan da suka mutu, kuma ina fatan wadanda suka ji rauni su samu sauki cikin gaggawa.,