Daga: Abbas Yakubu Yaura
Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya bayar da umarnin rufe duk wasu gidajen karuwai da ke a fadin jihar.
Ya kuma haramta sanya abin rufe fuska a wuraren taruwar jama’a domin tabbatar da tantance mutanen da suka dace a jihar.
Wannan dai ya biyo bayan tabarbarewar tsaro da ake fuskanta a jihar a ‘yan kwanakin nan.
DUBA WANNAN LABARIN: Najeriya Tana Baiwa ‘Yan Ta’adda Tukuicin Maimakon Kashe Su, Fani-kayode Ya Mayar Da Martani Kan Mutuwar Shugaban Al-Qaeda
Ya ba da wannan umarni ne a ranar Talata a Lokoja yayin wata ganawa da ya yi da dukkan sarakunan gargajiya na daya da na biyu ciki har da shugabannin kananan hukumomin jihar.
Bello ya kuma bayar da umarnin cirewa tare da rusa gidaje a Lokoja, Osara, Zango, Itobe, Obajana, da duk sauran yankunan jihar.
Ya bukaci kwamishinan kananan hukumomi da masarautu na jihar, shugabannin kananan hukumomi, shugabannin kungiyoyin kwadago, da jami’an tsaro da su gana da masu tuka babura masu kafa uku wato Keke Napep da babura masu kafa biyu domin samun cikakkun bayanai.
Gwamna Bello ya kuma bukaci dukkan sarakunan gargajiya da su kiyaye yankinsu tare da tabbatar da tsaftace duk wani lungu da sako na yankunansu.
“Tabbatar da zaman tare cikin lumana a yankinku alhakinku ne. Kuna da hakki na musamman na tabbatar da cewa duk lungu da sako na yankunanku sun kubuta daga aikata laifuka iri-iri,” in ji gwamnan.
Yayin da yake gargadin dukkan shugabannin kananan hukumomi da hukumomin tsaro da su ci gaba da gudanar da ayyukansu ba tare da tsoro ko fargaba ba, Bello ya yi gargadi ga ‘yan siyasa da kada su shiga duk wani abu da zai kawo cikas ga zaman lafiyar al’umma da kuma tsaron da suke samu a halin yanzu.
Ya kara da cewa “Bari na yi sanarwar gargadi ga dukkan ‘yan siyasa ba tare da la’akari da ra’ayin siyasa na nisantar duk wani abu da zai kawo cikas ga zaman lafiyar da muke samu a jihar ba.”