Gwamnan Jihar Ebonyi David Umahi ya tabbatar wa wasu fusatattun matasa a jiya Alhamis cewa gwamnonin shiyar kudu maso gabashin kasar nan za su mara musu baya a yaƙin da suke yi na neman kafa sabuwar kasa muddin ba a magance musu matsalar makasudin zanga-zangar tasu ba.
Mista Umahi ya bada wannan tabbaci ne yayin bada gudummawar shi a wani taron karin haske da tawagar Sadarwar Fadar Shugaban Kasa ta shirya a Abuja.
Kazalika ya bukaci matasan da su maida wukarsu kube, domin nan gaba ƙadan komai zai yi saiti inda ya bukace su da su baiwa gwamnonin nasu wa’adin watanni shida don samo bakin zaren lamarin.
“Na gudanar da wani taron masu ruwa da tsaki na kananan hukumomi 13, kana na sa an gudanar da addu’o’i na musamman” Cewar Umahi.
Daga bisani gwamnan ya jaddada cewa da yardar Allah gaskiya za ta yi halin ta nan gaba kadan, inda ya ce duk wani mugun mutum dake dora alhakin matsaloli kan shugaba Buhari asirinsa zai tonu.