Wani sabon rahoton masana na nuni da cewa, matsalar dumamar yanayi da ake fama da ita a duniya a yau na shafar hatta dabbobin da ke rayuwa a sararin samaniya, inda matsalar ke sauya musu zubin yanayin halittarsu.
Rahoton masanan na cewa, fasalin jikin tsuntsaye kamar akukuturu na kasar Australia da Zomaye na Turai na sauyawa saboda tasirin matsalar dumamar yanayi.
Sara Ryding mai bincike a Jamiar Deakin ta kasar Australia wadda ta jagoranci binciken dabbobin, na ganin lokaci ya yi da za a bai wa dabbobi kulawa domin su tafi daidai da zamani.
Wannan binciken da aka wallafa a ranar Talatar, ya yi nazarin wasu nazarce-nazarce na baya game da sauyin halittun dabbobi a dalilin sauyin yanayi a duniya, inda aka fara gano sauyin a cikin tsuntsaye.
Binciken ya tabbatar da cewa, ana samun kari wajen girman Aku na kasar Australia da kashi 4 cikin 100 bisa yadda yake a shekara ta 1871.
Haka ma an gano cewa, sauran tsuntsaye na wasu kasashen Turai sun kara girman jiki.