Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya ce barazanar nukiliya daga yakunan Ukraine da Asiya da Gabas ta Tsakiya sun sanya duniya cikin wani yanayi na kaico, duba da yadda cacat baka ke kara gaba a tsakani.
Antonio yayi wannan jawabi ne a zauren Majalisar Dinkin Duniya a jiya Litinin, yayin bude taron da aka dade ana jira don sake duba yarjejeniyar hana yaduwar makaman kare dangi ta shekaru 50 da suka gabata.
Wannan yunkuri na da nufin hana yaduwar makaman kare dangi wato Nukiliya, da kuma cimma yarjejeniyar nukiliyar ita kanta, ta fuskar mallaka da kuma amfani.
DUBA WANNAN LABARIN: rikicin PDP abu ne mai sauki akan na APC
Guterres ya shaidawa ministoci da jami’an diflomasiyya da dama da suka taru a zauren Majalisar cewa taron na duban taron na tsawon wata guda yana gudana “a daidai lokacin da hadarin nukiliyar da ba a taba ganin irinsa ba tun lokacin yakin cacar baka”.
Taron “wata dama ce ta fitar da matakan da za su taimaka wajen kauce wa wani bala’in da ka iya afkuwa a duniya baki daya, da kuma sanya mutane a kan sabuwar hanya zuwa duniyar da ba ta da makaman nukiliya”, in ji shi.
Duk da haka, Guterres ya yi gargadin cewa “makaman masu linzamin wani sabon ci gaba ne amma, takaita amfani da shi da kuma yaduwarsa zai taimaka wajen tabbatar zaman lafiya, duba da cewa yanzu haka akwai kusan makaman nukiliya 13,000 da ke cikin manyan makamai a duniya.
“Mun yi sa’a sosai zuwa yanzu. Amma sa’a ba dabara ba ce, Haka kuma ba garkuwa ba ce daga tashe-tashen hankulan yanki da ke taruwa zuwa rikicin nukiliya,” in ji shugaban na Majalisar Dinkin Duniya.
Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya ce Koriya ta Arewa na shirin yin gwajin makamin nukiliya karo na bakwai, yayin da Iran “ko dai ba ta so ko kuma ta kasa” amincewa da yarjejeniyar komawa kan yarjejeniyar nukiliyar ta 2015 da nufin karfafa shirinta na nukiliya, kuma Rasha ita ce ta yi burus da komai wajen ci gaba da farmakar inda bai kamata ta farmaka ba.