Shugaban kwamitin amintattu na jam’iyyar PDP, Sanata Walid Jibril, ya ce shirye-shirye sun yi nisa na hada dukkan fusatattun ‘ya’yan jam’iyyar da suka hada da gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, da sauran mambobin jam’iyyar.
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa bangaren da za a gana da su din dai sun kasance suna adawa da zaben Okowa maimakon Wike.
Abubuwa da dama basu yiwa uwar jam’iyyar dadi ba, musamman yadda ake ci gaba da zaman doya da manja a tsakanin yayanta, tun daga lokacin da Atiku ya kayar da Wike, a yayin neman cancantar zaman dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar.
KARAMTA WANNAN LABARIN: An Kama wani dilan kwaya a Kano
Sai dai Sanata Walid, wanda ya kasance dan majalisar dattawa a jamhuriya ta biyu a wata sanarwa da ya fitar a Kaduna ya ce babu wani abin damuwa domin jam’iyyar za ta yi duk mai yiwuwa wajen hada kan ‘ya’yanta.
Ya ce kwamitin ya shirya ganawa da shugaban jam’iyyar na jihar Ribas da sauran ‘yan jam’iyyar da suka yi kora domin sasantawa.
A cewarsa, abin da ke faruwa a babbar jam’iyyar adawa ta APC kan yan takara musulmai, nasu yafi sauki da fatan samun masara.
Ya bayyana jin dadinsa kan taron da gwamnonin jam’iyyar suka yi a baya-bayan nan da masu ruwa da tsaki domin sasanta ‘ya’yan jam’iyyar da suka ji ra’ayinsu, musamman gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike.