By Ishaq Dabai
Wani mutum mai matsakaicin shekaru, Kenneth Nwoha, ya kashe matarsa, Mercy, da dansa mai shekaru shida, Sampson a harin daya kai musu da adda.
Rahotanni sun bayyana cewa bayan kashe matarsa da dansa, Nwoha ya koma kan titi inda ya kuma kai hari kan wasu mutane shida.
Jaridar Dimokuradiyya ta samu labarin cewa lamarin ya faru ne a Unguwar Isiofumini Isieke dake cikin karamar hukumar Ebonyi ta jihar Ebonyi.Majiyoyi a yankin sun bayyana mamakinsu kan daukar matakin wanda ake zargin.
Majiyar tace ana zargin cewa mai yiwuwa mutumin ya samu tabin hankali ne jim kadan bayan ya farka daga bacci da safe kafin yaci gaba da kai farmaki tare da raba matarsa.
Daga cikin sauran mutane shida daya kashe, ya kai hari kan tituna sun hada da wani yaro dan shekara bakwai da wani mutum mai shekaru sittin.Har yanzu yana kai hari kan wadanda abin ya rutsa da su lokacin da ‘yan sanda suka isa wurin suka cafke shi
Jakakin ‘yan sandan jihar Loveth Odah ta tabbatar da faruwar lamarin.inda ta bayyana cewa wanda ake zargin ana duba lafiyarsa domin sanin halin da yake ciki kafin bayan abin da ya faru.
Ta kara da cewa mutane shida da wanda ake zargin ya kaiwa harin suna karbar magani a asibiti yayin da aka ajiye gawar mamacin a dakin ajiyar gawa.