A ranar Alhamis din nan ne Hukumar Yaki da masu yiwa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) ta ce tana binciken gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle kan zargin almundahanar Naira biliyan 70.
Hukumar ta EFCC ta kuma tabbatar da cewa har yanzu tana ci gaba da tsare tsohon ministan wutar lantarki, Sale Mamman, wanda jami’an hukumar suka kama a kwanakin baya bisa zargin almundahanar Naira biliyan 22.
KU KARANTA: Fubara Da FG Zasu Hada Kai Domin Bunƙasa Jihar Ribas
‘
Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa, Abdulrasheed Bawa, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a ranar Alhamis, inda ya bukaci ‘yan Najeriya da kada su bari a rudesu da furucin Matawalle na baya-bayan nan.
Idan dai za a iya tunawa, gwamnan ya tuhumi Bawa ne tare da bukatar ya ya Binciki mukarraban gwamnatin shugaba Buhari.
Sai dai Bawa wanda ya yi magana ta bakin Daraktan Hulda da Jama’a na Hukumar, Osita Nwajah, ya bayyana cewa bai kamata hukumar ta girmama Matawalle tare da mayar da martani ba amma ta yi hakan ne domin a daidaita lamarin.
“Abin takaici, ba cikin ikon Matawalle ba ne ya bayyana wa EFCC wanda za ta kama, kuma a ina. Wadanda ake zargi da ke hannun Hukumar yake da wata hujja cewa ga barayin daya kamata a kama.” Inji shi.
A wani labarin kuma: Kano: DSS Ta Tabbatar Da Cafke Matashi Baffah Hotoro