Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Kasa EFCC, ta gayyaci tsohon gwamnar jihar Nasarawa Tanko Al-Makura ofishin ta dake Abuja.
Al-Makura Wanda ya yanzu yake a matsayin Sanata, hukumar ta EFFC tayyace shi ne a jiya Laraba, tare da matar shi.
A cewar wani rahoto, an gayyaci Ma’auratan ne, domin amsa wasu tambayoyi kan wani zargi da keda alaka da al’mun-da-hanan wasu kudade, lokacin da ke Gwamnan jihar Nasarawa.
Biyo bayan tambayoyin, Tsohon gwamnan ya bayyana ra’ayin shi, sabanin zargin da a ke yi mishi, inda ya ce, Hukumar EFCC ba ta taba kamashi ba, face gayyatar shi da tayi.
KARANTA WANNAN LABARIN: IPOB ta yi barazanar dakatar da al’amuran cak, a yankin Kudu maso Gabas
Al-kura ya rike mukamin gwamnan jihar Nasarawa daga shekarar 2011 zuwa 2019, inda daga bisani aka zabe shi a mastayin Sanata Mai wakiltar Yankin Nassarawa ta Kudu, a majalissar Dattijan kasar nan.
A wani Labarin Kuma
Danladi Gyet Maude Mai rike da sarautar Gargajiya a jihar Kaduna, wanda Yan bindiga su ka yi garkuwa da shi a jihar Nasarawa, ya shaki iskar yanci.
Jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito yadda a ka yi garkuwa da basaraken, lokacin da ya jiyarci gonar shi, dake yankin Panda na jihar Nasarawa.
Amma wani Shaida ya bayyana wa Daily Trust a jiya Laraba cewa, an saki basaraken ne, da misalin karfe 9:30 na dare.
Sai dai shaidan bai bayyana cewa, ko an biya kudin fansa ba, kafin sakin Basaraken.
Basaraken mai shekaru 83 an sake shi ne awanni 48, bayan masu Garkuwa da mutane sun yi awon gaba dashi, inda aka ganshi tare da wasu mabiyan shi, a fadar shi a daran jiya Laraba.
Sarki Maude na daya daga cikin Sarakunan dake jihar Kaduna, masu yawaicin shekaru.
Comments 1