Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna a ranar Juma’a ya yi zargin cewa Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele ya bullo da tsarin sake fasalin Naira ne domin taimakawa jam’iyyar PDP ta lashe zaben 2023 ne, kamar yadda Channels TV ta rawaito.
“PDP ce ta nada Emefiele gwamnan babban bankin kasar tun asali. Don haka kar mu manta daga inda ya fito,” El-Rufai ya fadi haka ne a wata hira da manema labarai jim kadan bayan da kotun koli ta bayar da umarnin a ci gaba da aiki da tsofaffin takardun kudi na N200, N500, da N1,000 har zuwa ranar 31 ga watan Disamba, 2023.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yanzu-Yanzu: Jihohin PDP Bakwai Sun Janye Karar Da Suke Kalubalantar Nasarar Tinubu
Kotun kolin ta kuma soke manufar gwamnatin tarayya na sake fasalin Naira, inda ta bayyana hakan a matsayin cin fuska ga kundin tsarin mulkin shekarar 1999.
Kotun ta ce manufar ta sa wasu mutane suna yin fatauci a wannan zamani da nufin ci gaba da rayuwa.
Jihohi 16 karkashin jagorancin Kaduna, Kogi da Zamfara sun yi wa kotun kolin rokon ta ruguza tare da ajiye manufofin FG a gefe kan cewa tana wahalar da ‘yan Najeriya da ba su ji ba ba su gani ba.
Da yake zantawa da manema labarai bayan yanke hukuncin, El-Rufai wanda ya shaida hukuncin tare da yan uwansa gwamnonin APC kamar Yahaya Bello na jihar Kogi da Bello Matawalle na jihar Zamfara, ya ce gwamnan babban bankin CBN ya yaudari shugaban kasa Muhammadu Buhari don aiwatar da manufar.
“Shi (Emefiele) shine wanda suka fitar da wannan manufa tare domin taimakawa jam’iyyar PDP ta lashe zaben 2023 kuma suka yaudari shugaban kasa da tunanin cewa za’a iya cire Naira Tiriliyan 2 da suke zagayawa a sake buga wasu kudin cikin watanni uku. Babu wata kasa a tarihin duniya da ta yi hakan,” in ji gwamnan Kaduna.
A wani labarin kuma, El-Rufa’i Ya Magantu Bayan Kotun Koli Ta Yanke Hukunci Kan Tsoffin Kudin Naira
Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya ce hukuncin da kotun koli ta yanke ya tabbatar da matsayinsa game da sake fasalin tsarin naira da babban bankin Najeriya ya aiwatar.
Jim kadan bayan hukuncin da kotun kolin ta yanke, El-Rufai ya karyata ikirarin cewa matsayar sa a kan manufar sake fasalin naira na da nasaba da siyasa.