Jihohi bakwai karkashin jam’iyyar PDP, wadanda suka shigar da karar gwamnatin tarayya a kotun koli suna kalubalantar nasarar da zababben shugaban kasa, Bola Tinubu ya samu a zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar Asabar, sun dakatar da karar.
A karar da suka shigar da babban Lauyan Jihohin Bakwai da kuma Babban Lauyan Tarayya a matsayin wanda ake kara, Jihohin bakwai da suka hada da Adamawa, Akwa Ibom, Bayelsa, Delta, Edo da Taraba da kuma Sokoto ya bukaci kotun koli ta sa baki a zaben shugaban kasa da aka kammala, yana mai cewa shelanta Tinubu bai bi tanade-tanaden dokar zabe ta 2022 da kuma ka’idojin hukumar zabe mai zaman kanta ba, kamar yadda wani rahoton Thisday Live ya bayyana.
KARANTA WANNAN LABARIN: El-Rufa’i Ya Magantu Bayan Kotun Koli Ta Yanke Hukunci Kan Tsoffin Kudin Naira
Karar dai tana kalubalantar gazawar INEC wajen shigar da sakamakon zaben zuwa IReV wanda akayi amfani da BVAS. Sun kuma bayyana fargabar yiwuwar tabarbarewar zaman lafiyar jama’a da rashin biyayya ga al’umma.
Sanarwar dakatarwa, wacce lauyansu, Mista Mike Ozekhome, ya sanya wa hannu a ranar Juma’a, ta ce, “Ku lura cewa masu shigar da kara sun dakatar da wannan kara da ake yi wa wanda ake kara a nan….”
A wani labarin kuma, Kasar Burundi Zata Tura Dakarun Soji Zuwa Gabashin DR Congo
Kasar Burundi za ta tura sojoji 100 zuwa gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango a ranar Asabar mai cike da tashin hankali a matsayin wani bangare na rundunar yankin, kamar yadda wani babban jami’in sojan Burundi ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP.
Kungiyar kasashen gabashin Afirka bakwai ta tura dakaru a karshen shekarar da ta gabata a gabashin DRC, wacce ke fama da bullar mayakan sa-kai da suka hada da ‘yan tawayen Movement (M23) a ranar 23 ga watan Maris.