Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya ce hukuncin da kotun koli ta yanke ya tabbatar da matsayinsa game da sake fasalin tsarin naira da babban bankin Najeriya ya aiwatar.
Jim kadan bayan hukuncin da kotun kolin ta yanke, El-Rufai ya karyata ikirarin cewa matsayar sa a kan manufar sake fasalin naira na da nasaba da siyasa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kasar Burundi Zata Tura Dakarun Soji Zuwa Gabashin DR Congo
A maimakon haka, ya ce manufar ta jawo wa ‘yan Najeriya wahalhalu da ba a taba gani ba.
“Yau rana ce ta farin ciki ga dukkan ‘yan Najeriya; kotun koli ta sassauta mana. Cewa duk rokon da muka yiwa kotu sun [amsa],” inji shi.
El-Rufai ya ce: “Bamu amince da Buhari kan aiwatar da manufofin ba; muna godiya ga kotun da ta yanke hukuncin baki daya ta hanyar umurtar gwamnatin tarayya ta ba da izinin tabbatar da zagayawar tsoffin takardun naira har zuwa ranar 31 ga watan Disamba.”
“Mun je kotu ne, ba don zaben gama-gari ba, sai don ‘yan Najeriya na fama da wahalhalu da ba a taba ganin irinsa ba saboda manufar sake fasalin Naira.”
A cewarsa: “An yi amfani da tsarin ba bisa ka’ida ba kuma ana aiwatar da shi. Rashin jituwar mu da manufofin ba tawaye ba ne illa gyarawa.”
Tun da farko dai El-Rufai, Gwamnan Kogi Yahaya Bello da takwaran su na Zamfara Bello Matawalle sun maka gwamnatin tarayya kara a gaban kotu kan batun sauya fasalin Naira da nufin kawar da N200, N500, da N1000.
Hukuncin, idan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya zartar da shi, yana nufin cewa tsofaffin takardun kudi za su yi aiki tare da sabbin takardun Naira har zuwa ranar 31 ga watan Disamba.
A wani labarin kuma, Gwamnatin Yobe Ta Sake Duba Lokacin Zirga-Zirgar Masu Adai-Daita Sahu a Kananan Hukumomi 17
Gwamnatin jihar Yobe ta sake duba sa’o’in ya nayin zirga-zirgar ma’aikatan babur mai kafa uku a fadin kananan hukumomi 17 na jihar.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun mai baiwa gwamna shawara na musamman kan harkokin tsaro Dahiru Abdulsalam.