A daren Talatar da ta gabata ne fadar shugaban kasa ta mai da martani akan wata zanga-zangar da wasu da suka kira kansu “Masu ruwa da tsakin jam’iyyar APC da suka damu da yadda ake gudanar da gwamnatin shugaba Buhari”, inda suka bukaci Shugaba Buhari da ya kori wasu na hannun damansa daga sha’anin tafiyar da mulkin kasar.
A martanin da fadar shugaban kasar ta mayar dangane da zanga-zangar da aka yi, na cewa wasu ne kawai suka kitsa wannan zangazangar don wata manufa.
An ruwaito mai magana da yawun shugaba Buhari, Malam Garba Shehu yana cewa, nan gaba akwai yi wuwar kara shaida makamancin irin wannan.
Ya yi zargin da a nan birnin Abuja da akwai shaguna na musamman da aikinsu shi ne bada hayar kwalaye tare da masu zanga-zangar.
Garba Shehu ya ce, ya kamata irin wadannan mutanen su kwana da sanin cewa, Shugaba Buhari ba zai taba fadawa irin wannan tarkon da su ke danawa ba.