Farashin iskar gas a shekara zuwa shekara ya karu da kashi 101.17 a watan Agustan 2022 idan aka kwatanta da Agustan 2021, in ji Hukumar Kididdiga ta Kasa.
Matsakaicin farashin iskar gas mai nauyin kilogiram 5 ya karu daga N4,397.68 a watan Yuli zuwa N4,456.56 a watan Agusta.
Hukumar ta NBS ta bayyana hakan ne a cikin rahoton ta mai taken Cooking Gas Watch Watch da ta fitar Talatar nan a Abuja.
An lura cewa farashin a watan Agusta ya nuna karuwar kashi 1.34 a kowane wata daga abin da aka samu a watan Yuli.
KARANTA ANAN: Bashin Da Ake Bin Najeriya Ya Haura Biliyan Dubu 40
Rahoton ya kara da cewa Taraba ta kasance mafi girman farashin N4,925.44, akan iskar gas mai nauyin kilogiram 5, sai Adamawa inda aka sayar da ita N4,920, sai kuma jihar Legas inda aka sayar da ita kan N4,782.50.
Ya kuma bayyana cewa jihar Katsina ta samu mafi karancin farashin N4,020 a watan Agusta, sai Ogun da Yobe a kan N4,057.14 da kuma N4,078.46, bi da bi.
Bincike na shiyyar yankunan ya nuna cewa Arewa ta Tsakiya ta sami mafi girman farashin dillali na N4,615.95 na iskar gas mai nauyin kilogiram 5, sai kuma Arewa maso Gabas a kan N4,548.03.
Arewa-maso-Yamma ta samu mafi karancin farashi akan N4,285.51.
Rahoton ya kara da cewa Taraba ta kasance mafi girman farashin N4,925.44, akan iskar gas mai nauyin kilogiram 5, sai Adamawa inda aka sayar da ita N4,920, sai kuma jihar Legas inda aka sayar da ita kan N4,782.50.
Ya kuma bayyana cewa jihar Katsina ta samu mafi karancin farashin N4,020 a watan Agusta, sai Ogun da Yobe a kan N4,057.14 da kuma N4,078.46, bi da bi.
A wani labarin kuma: Ku tabbatar anyi Zaɓen 2023 cikin Zaman Lafiya – Kiran Limamai ga Ƴan Siyasa
Majalisar Limamai da Malamai reshen Jihar Kaduna, ta yi kira ga ƴan siyasa da Musulmi baki daya da su gudanar da rayuwarsu cikin kwanciyar hankali ba tare da nuna kyama ba, a daidai lokacin da ake fara yakin neman zaben 2023.
Mataimakin Babban Sakatare-Janar Imam Musa Tanimu da jami’in hulda da jama’a na majalisar, Dokta Abdullahi Maikudi, a wani taron Manema Labarai na haɗin gwiwa, jiya a Kaduna, sun kuma yi kira ga ‘yan kasar da su guji maganganun da ka iya haifar da karya doka da oda.