Farfesa Kabiru Bala ya shiga Ofis a matsayin shugaban Jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya. Inda ya yi alkawarin dawo da martabar Jami’ar da aka santa da shi a da.
Farfesa Bala, wanda ya karbi ragamar shugabancin Jami’ar har na tsawon shekara biyar, ya yi alkawarin ganin ya yi bitar tsarin koyarwa na jami’ar da kuma bin diddigin asalin tubalin da aka gina Jami’ar domin ganin ya kawo mata ci gaba.
Farfesan ya ce akwai aiki ja a gaba wajen ganin an tafi da zamani, inda ya ce rabon Jami’ar Ahmadu Bello da shirya taron masana ta dade. Inda ya ce na karshe da aka yi shi ne a 1982, lokacin shugabancin Farfesa Ango Abdullahi.
Ya ce ya kamata a ce wannan tsarin ya dawo.