Gwamnan Jihar Zamfara Bello Muhammad Matawalle Ya ce akwai yan fashin daji sama da dubu talatin a Jihar Zamfara da karin wasu Jihohi arewa biyar.
A Cewar Gwamnan, akwai sansanonin yan fashin daji sama da dari a fadin jihar, wanda kowannen su ke dauke da mayaka sama da dari uku dake cin karen su babu babbaka.
Matawalle yana wannan tonon asiri nw ta bakin sabon kwamishinan yada labaran shi Alhaji Ibrahim Magaji Dosara yayin karin haske wa manema labarai a Jihar Kaduna.
Jihohin da wadannan mutane suke, kamar yadda ya bayyana sun hada da Zamfara din ita kan ta da Sokoto da Kebbi da Katsina da Kaduna da Kuma Jihar Neja.
Ya ce wannan al’amari na ci gaba da fin karfin gwamnatin tarayya ganin cewa dakarun dake yaki da wadannan yan ta’adda ba su taka kara sun karya ba.
Inda ya ce a halin da ake ciki mayakan soji dubu shida ne kachal ke yaki a fadin shiyar arewa maso yamma inda nan ne al’amarin fashin dajin yafi kamari.