Babbar kotun jihar Legas ta ware ranar 17 ga watan Fabrairu domin yanke hukuncin amince wa ko akasin haka dangane da bayyanar shugaba mai kula da hada-hadar bankin Zenith da ke birnin Ado-Ekiti, Mr Johnson Abidakun a gaban kuliya domin bayar da shaida kan shari’ar da ake yi wa tsohon gwamnan jihar EKiti, Ayo Fayoshe.
EFCC ta gabatar da Abidakun domin maye gurbin matukin motar daukar kudi mai sulke ta bankin na Zenith da ke Ado-Ekiti, Adewale Aladegbola wanda ya bayar da shaida tun da farko.
Hukumar EFCC dai ta gurfanar da shi ne a ranar Litinin kan tuhume-tuhume 11 ciki har da laifukan cin hanci da rashawa da halarta kudin haram da sauransu.
Ana kuma zargin shi da karbar dala miliyan biyar daga hannun tsohon ministan tsaron kasar Musiliu Obanikoro, wanda ta ce ya yi amfani da su wajen yakin neman zaben gwamnan jihar a shekarar 2014.
Sai dai tsohon gwamnan ya musanta duka wadannan tuhume-tuhumen.