Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya sanya hannu kan dokar haramta zirga-zirga da Babur din ‘yar kurkura daga karfe 7 na dare zuwa 6 na safe a kowacce rana.
Kwamishinan shari’a na jihar, Alhaji Ahmed El-Marzuq shi ne ya bayyana hakan jim kadan da gwamnan ya sanya hannu kan dokar a gidan gwamnati dake Katsina.
Kwamishinan ya ce dokar za ta fara aiki ne daga ranar 20 ga watan Janairun 2020.
Alhaji Ahmed El-Marzuq ya ce dokar amma ba ta shi jami’an tsaron ‘yan sanda, sojoji, FRSC, NDLEA, Kwastan, NSCDC, da sauran jami’ai na tsaro ba.
Ya tabbatar da cewa gwamnati ta dauki wannan matakin ne duba da yadda kowanne irin garkuwa da jama’a da ake yi yana da alaka da amfani da Babura, da kuma ‘yar kurkura, inda ya ce dokar ba kawai ta takaita ga kananan hukumomi takwas bane da abin ya fi kamari ba, ya shafi dukkanin jihar.
Kwamishinan ya ce duk wanda aka kama ya sabawa wannan dokar, za a rufe shi a gidan yari na shekara daya ko kuma a ci shi tara, ko a hada masa duka.