Gwamnatin tarayya ta fitar da jerin sunayen mutane 20 da za su fafata a matsayin sabon babban akanta janar na tarayya, AGF, a cewar wata kafar intanet, TheCable.
‘Yan takarar guda 20, a cewar wata takardar da gwamnati ta fitar, an zabo su ne daga ma’aikatu, da hukumomi, MDAs.
KARANTA WANNAN LABARIN: Noma Shine Hayar Magance Matsalar Hauhawar Farashin Kayayyakin Abinci – Dattijon Kasa
Ku tuna cewa an kama Ahmed Idris, tsohon AGF ne a Kano bayan ya kasa amsa gayyatar da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati, EFCC ta yi masa na amsa tambayoyi kan zargin almundahanar Naira biliyan 109.
Bayan kwanaki biyu, ministar kudi, kasafin da tsare-tsare ta kasa, Misis Zainab Ahmed ta dakatar da Idris har sai baba ta gani “ba tare da biya ba”.
Chukwunyere Anamekwe, wanda aka zaba ya maye gurbin Idris a matsayin mukaddashin, an kuma cire shi.
A cikin takardar, gwamnati ta bayyana cewa, jerin sunayen ya biyo bayan rahoton da hukumomin yaki da cin hanci da rashawa suka bayar kan tantance masu son shiga takarar da suka nemi shiga cikin tsarin nadin na AGF.
Ta ce a yau 9 ga watan Janairu za a fara aikin tantance jerin sunayen ‘yan takarar.
“Saboda haka, ‘yan takarar da aka tantance za su zo ne domin gudanar da aikin karramawar da aka shirya gudanarwa daga ranar Litinin 9 zuwa Laraba 11 ga watan Janairu, 2023 a dakin taro na Olusegun Obasanjo, ofishin shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya, sakatariyar gwamnatin tarayya, Phase lI, Abuja. tsakanin karfe 8.00 na safe zuwa 4:00 na yamma kowace rana,” in ji da’irar.
Jerin sunayen wadanda aka tantance sun hada da Mohammed Aminu Yara’abba (Hukumar kashe gobara ta tarayya); Danladi Zakowi Comfort (Interior); Mahmud Adam Kambari (Arewa maso gabae Dev. Comm); Mohammed Magaji. M. Doho (Interior); Waziri Amos Samuel (Cibiyar Noma da Karkara); da Madein Oluwatoyin Sakirat (OHCSF).
Sauran sun hada da Adaramoye Joseph Oluwole (kula da harkokin jinkai); Isa Abubakar (Science, Tech & Innovation); Ogunsemowo Oladipupo Olakunle (Muhalli); Egbokale Kadiri Charity (Nig. Football Federation); da lbrahim Sa’adiyya Jibo (Hukumar Kula da iyakokin kasa).
A wani labarin kuma,An Cafke Guda Cikin Wadanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Fasinjojin Jirgin Kasa
Kwamishinan yada labarai na jihar Edo, Chris Nehikhare, ya bayyana cewa jami’an tsaro sun cafke daya daga cikin wadanda ake zargin masu garkuwa da mutane ne da hannu wajen yin garkuwa da fasinjoji 32 a tashar jirgin kasa ta Igueben.
Nehikhare ya bayyana haka ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a birnin Benin a karshen mako.