Aisha Bichi, matar shugaban hukumar ƴan sandan farin kaya (DSS), Yusuf Bichi, ta bayar da umurnin a cafke ɗan takarar gwamnan jihar Kano na jam’iyyar NNPP, Abba Kabir Yusuf, sannan ta hana shi shiga jirgin Max Air daga Kano zuwa Abuja a daren ranar Lahadi.
Jaridar Daily Nigerian ta rahoto cewa rigimar ta fara a wajen shiga ɓangaren manyan baƙi na musamman na tashar jirgin sama ta Aminu Bello Kano, lokacin da tawagar motocin ɗan siyasar suka haifar da cunkoso, wanda hakan ya ɓatawa motocin Aisha Bichi lokaci wajen samun shiga wajen.
KARANTA KUMA: Noma shine hanyar magance hauhawar farashin abinci -Dattijon ƙasa
Majiyoyi sun tabbatar da cewa lamarin ya fusata Aisha Bichi inda jami’an tsaron ta suka fara dukan mutane da farfasa motoci saboda an ƙi mutunta ta.
Shaidun gani da ido sun bayyana cewa bayan ƙura ta lafa, Abba Kabir Yusuf ya shiga wurin domin ya sameta a matsayinta na ƙawar matarsa, sannan yayi mata ƙorafi akan halin rashin dacewa da mutanenta suka nuna.
“Abba yana zuwa wajenta ta fara zaginsa ta uwa ta uba. Duk da cewa darektan hukumar na jiha yayi ƙoƙarin yaga ta huce, ta cigaba da zage-zagen, inda take cewa ba zata bari ya zama gwamna ba. A cewar shaidar gani da ido.
Lamarin ya ƙara ta’azzara ne lokacin da ta hango wani daga cikin ƴan tawagar Abba Yusuf yana ɗaukar bidiyon rigimar da wayar sa.
Tana hango Kilo yana ɗaukar bidiyo, nan da nan ta bayar da umurnin jami’an ta halaka shi, inda take cewa ku kashe shi, kuma ba abinda zai faru.
“Ta kuma yi alwashin cewa ba zata bari Abba ya shiga jirgi ɗaya tare da ita ba a cikin daren. A na cikin hakan sai darektan hukumar na jiha ya roƙi Abba da ya fasa tafiyarsa ya koma gida.
A yayin da Abba ya haƙiƙance sai ya shiga jirgin, sai ga ƙarin jami’an DSS sun zo filin zirgin inda suka zagaye wajen. Wasu manyan-manyan jami’ai suka shigo wajen suka gayawa Abba Cewa an kama shi. Inji majiyar.
Lokacin muna soyayya har kuɗin mashin da sauransu nake ba ta, Saurayin Rahama Sadau na ƙuruciya
Wani matashi wanda Freedom Radio ta yi hira da shi ya bayyana cewa sun taba soyayya da jaruma Rahama Sadau amma a baya.
Kamar yadda yace, lokacin makarantar sakandare su daya a shekarar 2004 kuma wurin zamansu daya.