Akalla mutane 81 aka kashe a fadan da aka gwabza tsakanin Tajikistan da Kyrgyzstan a cikin wannan mako, a tashin hankalin mafi muni da kasashen suka gani cikin shekaru da dama, yayin da kasashen duniya suka yi kira da a kwantar da hankula.
Sai dai kuma halin da ake ciki a kan iyakar da ake gwabzawa tsakanin makwaftan kasashen tsakiyar Asiya an samu kwanciyar hankali a yammacin ranar Lahadin nan, a cewar hukumomin Kyrgyzstan.
Rikici ya barke a tsakanin tsoffin jamhuriyar Soviet guda biyu, yayin da kusan rabin iyakarsu mai tsawon kilomita 970 (mil 600) ya rage.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Tajikistan ta fada a ranar Lahadin nan cewa an kashe ‘yan kasarta 35, wanda shi ne adadin farko da suka mutu a hukumance tun bayan barkewar rikicin a ranar Laraba.
KARANTA KUMA: Wani Rikicin Iyaka Ya Haddasa Wata Gobara Mai Tsanani
A shafinta na Facebook, ma’aikatar harkokin wajen Tajik ta kuma bayar da rahoton jikkatar mutane 25, ta kuma ce fararen hula ne, mata da kananan yara na cikin wadanda abin ya shafa.
Ma’aikatar ta zargi sojojin Kyrgyzstan da kashe mutane 12 a wani harin da jirgi mara matuki ya kai a wani masallaci, da kuma wasu shida a harin da aka kai a wata makaranta.
Kamfanin dillacin labarai AFP ya rawaito cewa ba ta iya tabbatar da ikirarin da kanta ba.
A halin da ake ciki Kyrgyzstan ta ce a ranar Lahadi akalla mutane 46 ne suka mutu a yankin Batken da ke kan iyaka da kudancin kasar, kuma 140 sun jikkata.
An kwashe dubunnan mutane daga yankunan kan iyakar Kyrgyzstan a cikin kwanakin da suka gabata, a cewar kungiyoyi masu zaman kansu.
Tashar talabijin ta Channels ta rawaito cewa, Kyrgyzstan ta ayyana ranar 19 ga watan Satumba a matsayin ranar makoki ta kasar.
A wani labarin kuma: Shugaba Buhari Zai Kaddamar Da Cibiyar Kula Da Cutar Daji A Kano
Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kaddamar da cibiyar kula da cutar daji a Kano na biliyoyin naira kafin karshen Oktoba, 2022.
Kwamishinan lafiya na jihar, Dr. Aminu Ibrahim Tsanyawa wanda a ranar Lahadin nan ya bayyana cewa tuni an kusa kammala ginin cibiyar kula da lafiyar ta duniya da gwamnatin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ke ginawa.
Comments 1