Wani manazarci a Najeriya Dakta Zakariyya Adam ya bayyana cewa tsohon Gwamnan Jihar Kano Dakta kuma shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa Abdullahi Umar Ganduje ruwan sanyi ne dafa moɗa.
Dakta Zakariyya ya ce sau da dama tsohon gwamnan na Kano na nuna halin ko oho da wani da yake takun saƙa da shi toh amma daga bisani yakan dafa shi da ruwan jikinsa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Jam’iyar NNPP Ta Dakatar Da Kwankwaso Daga Shiga Harkokin Jam’iyar Akan Zargin Yi Mata Zagon Kasa
Manazarcin ya buga misali da zaman doya da manjar da Ganduje ya yi da Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, inda ya ce tsohon gwamnan na Kano ya yi shakulatin ɓangaro da shi amma daga bisani shi ke da nasara.
Ya ƙara da cewa duk da kasancewar Mai Martaba Muhammadu Sanusi II mai fikira ne da da sanin ya kamata, toh amma Ganduje ya nuna masa cewa idan ka iya ruwa toh tabbas ba za ka iya taɓo ba, ta hanyar tuɓe masa rawani a kujerar Sarkin Kano na biyu.
Da ya taɓo sa-toka-sa-katsin Ganduje da tsohon gwamnan Kano Dakta Rabiu Musa Kwankwaso kuwa, manazarcin ya ce shugaban APCn na yanzu ya nuna masa cewa kowane bakin wuta da nasa hayaƙi inda ya yi amfani da dokar farko ta cikin littafin 48 Laws of Power dake cewa kada ka nunawa mai gidanka ka fi shi iyawa.
Dakta Zakariyya ya ce wannan ɗabi’ar ce ta sanya Kwankwaso sakankancewa har ta kai ga Ganduje ya shammaceshi da cewa wuta tun tana ƙanƙanuwa ake kasheta.
Wani abinda ya ɗauki hankali a baya-bayannan kuma shine alamarin Tsohon Gwamnan na Kano da kuma matashiyar ƴar siyasa Maryam Shettima wacce aka fi sani da Maryam Shetty da shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya bayyana sunanta a matsayin wacce majalisa za ta tantance a matsayin Minista.
Kwatsam daga bisani aka ga shugaban ƙasar ya cire sunan Shetty daga jerin sunayen ministocin nasa, lamarin da aka danganta hannun tsohon Gwamnan dumu-dumu wajen cireta cikin wani abinda aka kira da bashin gaba.
Idan za a iya tunawa dai a shekara ta 2019 ne Maryam Shetty ta wallafa wani rubutu a shafinta na Facebook dake kalubalantar zargin wata badaƙalar kuɗi da aka yiwa Ganduje da kuma maguɗin zaɓe, lamarin da Ganduje ya kawar da kai tun daga wanchan lokaci.
Amma manazarci Dakta Zakariyya ya alaƙanta shirun da Ganduje ya yi da kundin doka ta 35 dake cikin wanchan littafi da muka bayyana a baya mai nuni da cewa “Nazartar lokacin kai farmaki ga abokin hamayya na da matukar muhimmanci” lamarin da hakan ya yi wa Ganduje tasiri.
Daga bisani Dakta Zakariyya ya buƙaci malamai da daliban ilmin kimiyyar siyasa da su sanya salon Dakta Abdullahi Umar Ganduje cikin tsarin koyon Digirin digirgir wato PhD ta inda ya ce hakan zai taimaka wajen tinƙarar abokan hamayya a siyasance.