Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya ziyarci iyalan mutane 19 da suka yi hatsarin mota tsakanin babbar hanyar Zaria zuwa Kano, a kauyen Tusguri da ke unguwar Sanda, a karamar hukumar Bunkure.
Ganduje ya bayar da kudi Naira Dubu Dari Biyu (Naira 200,000) ga kowanne iyalan wadanda suka mutu a kan hanyarsu ta dawowa daga Ilorin.
Wannan na kunshe cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labaran gwamna Abba Anwar ya aikowa JARIDAR DIMOKURADIYYA a ranar Lahadin nan.
Sanarwar ta ccme “Mun samu labarin rasuwar cikin kaduwa, muna kuma addu’ar Allah Subhanahu Wata’ala ya gafarta musu dukkan kurakurensu, ya saka mu a Aljannah,” inji shi.
Gwamnan ya umurci shugaban karamar hukumar ya rubutawa gwamnatin jihar da bukatar gina makarantar firamare a yankin. Wanda yayi alkawarin gaggauta daukar mataki.
Haka kuma Don kuma taimakawa al’ummar yankin wajen noman rani, “Ina mai tabbatar muku da cewa, gwamnatin tarayya ta sa baki wajen noma rani, wannan garin zai kasance cikin shirin.
Abba Anwar
Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamnan Jihar Kano.
Lahadi, 24 ga Yuli, 2022