Gwamna-Ganduje-na-jihar-Kano.

Ganduje Ya Yi Kira Ga ‘Yan Adawa Su Zo A Ci Gabantar Da Kano

‘Yan mintoci kadan da kotun koli ta yanke hukunci na tabbatar da nasarar Gwamna Abdullahi Umar Ganduje a matsayin gwamnan Jihar Kano, gwamnan ya mika godiyarsa ga Allah bisa wannan nasara, inda ya yi kira ga ‘ya adawa da su zo a hada hannu wajen ciyar da jihar gaba.

A sanarwar da Sakataren watsa labarai na gwamnan, Abba Anwar ya fitar, ya bayyana cewa gwamnan ya ce; “Muna mika godiyarmu ga Allah bisa nasarar da muka samu a kotun koli na tabbatar da hukuncin kotun sauraren kararrakin zabe da na kotun daukaka kara. Sannan muna godiya ga al’ummar Kano bisa yadda suka kasance cikin zaman lafiya a yayin gudanar da lamuransu.” In ji gwamnan.

Sannan har wala yau gwamnan ya yi kira ga dukkanin mutanen da suka bada gudummawa wajen wannan nasarar da ya samu, inda ya jaddada cewa; “Duk wanda ya yarda da Allah, a koyaushe zai rika ganin haske a farko da tsakiya da kashen lamuransa cikin kowanne yanayi.”

Gwamnan ya kara da cewa; “Muna kuma mika godiya ga dukkanin Alkalan da suka gudanar da aikinsu na shari’a bisa turbar dimokuradiyya. Wannan ya tabbatar da yadda bangaren shari’a ke cin gashin kansa da kuma kokarinsu na bunkasa dimokuradiyya. Sun cancanci jinjina.”

Gwamna Ganduje ya yi kira ga ‘yan hamayya da cewa; “Ina mai kira ga ‘yan hamayya da su zo su hadu da mu domin kawo wa jihar ci gaba. Muna da ayyukan ci gaba da yawa a kasa. Kuma zamu bullo da wadansu. Shirinmu na bayar da ilimi kyau yana bukatar hannun kowa. Sannan tsaronmu na bukatar taimakon kowa.”

Jim kadan da tabbatar da nasarar Ganduje a matsayin gwamnan Kano da kotun koli ta yi  gidan gwamnatin Kano ta cika da al’umma wadansu suka rika yin murnar nasarar da suka samu. Kuma a wadansu titunan Kano ma an samu wadanda suka fito domin nuna murnar nasarar Gwamna Ganduje.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *