Manoman shinkafa da ‘yan kasuwa a jihar Sakkwato da ke arewa maso yammacin Nijeriya sun ce sam barka domin sun ga tasirin hana shigo da shinkafa da rufe kan iyakoki da gwamnati ta yi.
Sai dai kuma sun koka kan yadda ake fasa kaurin shinkafa ‘yar waje a cikin jihar mai makwabtaka da Nijar, dalilin da suka ce ke sa kasuwar shinkafa ‘yar gida ke ja da baya.
A hannu guda su kuma mutanen gari kokawa suke da tsadar farashin shinkafar ‘yar gida da aka gyare aka cirewa tsakuwa.