Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya mikawa mataimakinsa Dr. Nasiru Yusuf Gawuna da tsohon kwamishinan kananan hukumomi Murtala Sule Garo Fom na tsayawa takara gwamna da mataimaki a jam’iyyar APC.
Hakan na nufin cewa ya zabe su matsayin yan takarar da zasu tsayawa jam’iyyar APC a zaben baɗi.
Gwamna Ganduje tabbatar da hakan ne a yau, yayin wani taron yan jam’iyyar da aka gudanar a dakin taro na Africa House dake gidan gwamnati.
Ganduje ya ce ya dauki wannan mataki ne bayan dogon nazari da kuma tuntubar na gaba, wanda suka tabbatar da cancantar su, tare da fatan ganin sun samu nasara.
Yanzu haka dai Dr Nasir Yusuf Gawuna shine ɗan dan takarar Gwamna a APC, yayin da Hon. Murtala Sule Garo ke matsayin mataimakinsa.
Kazalika a yayin zaman na yau mambobin majalisar zartarwar jiha, sun sake jaddada bukatar su ga Gwamna Ganduje kan ya tsaya takarar Sanatan Kano ta Arewa.
Dan majalisar tarayya mai wakiltar Doguwa da Tudun Wada shine ya jagoranci rokon, bayan da ya mikawa gwamnan Gon dinsa na takarar.