Hukumar Kula da Inshorar al’umma ta kasa NSITF ta shaida wa Majalisar Dattijai cewa, Gara ta cinye takardun da ke kunshe da bayanai kan yadda hukumar ta kashe Naira biliyan 17.158, wanda har yanzu babu duriyarsu.
A shekara ta 2018 ne rahotan binciken kudaden da aka kashe ya bayyana cewa, Asusun na NSITF ya yi amfani da bankunan Skye da First Bank wajen tura Naira biliyan 17.158 zuwa ga asusun bankunan wasu daidaikun mutane da kamfanoni daga watan Janairu zuwa Disambar shekarar 2013.
Rahotanni sun bayyana cewa, an dai gaza tantance ainihin makasudin aika makuden kudaden zuwa ga wadannan bankunan na daidaikun mutane da kamfanoni biyo bayan ikirarin NSITF na cewa, Gara ta cinye takardun da ke fayyace musabbabin aika kudaden.
Ofishin babban mai binciken kudaden na kasa Najeriya ya gabatar da tambayoyi 50 game da zarge-zargen barnatar da dukiyar kasa da hukumar ta NSITF ta yi, lamarin da yanzu haka ke gaban kwamitinin kula da asusun kudaden al’umma na Majalidar Dattijai don ci gaba da gydanar da bincike.
Kwamitin ya tuhumi tsoffin shugabannin NSITF da suka gabata da kuma na yanzu, amma babu wanda ya iya bada wani gamsasshen bayani dangane da ainihin dalilin fitar da wadannan kudade.
Manaja Darektan NSITF na yanzu, Dr. Michael Akabogu ya bayayna cewa, babu wasu takardu da suke da nasaba da kudaden da ake bincike a kai da ya tarar a ofishinsa.