Fitaccen dan jarida, Dele Momodu, ya auna rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar PDP, inda ya ce gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ba zai bar babbar jam’iyyar adawa ba.
An dai samu rashin jituwa a jam’iyyar PDP tun bayan fitowar tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar a zaben 2023 mai zuwa.
Ana kyautata zaton gwamnan ya fusata ne saboda da cewa Atiku ya amince da Gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta a matsayin abokin takararsa.
Sai dai Momodu ya yi ikirarin cewa Wike ba zai yi watsi da jam’iyyar PDP ba saboda shi dan siyasa ne mai bin ka’ida, inda ya kara da cewa wasa da hankali ne kawai yake yi.
Zamu Karfafa Alaka Da Koriya Ta Arewa Don Magance Barazanar Abokan Gaba–Putin
“A gani nai, gwamna Wike mutum ne mai kishin kwarai da gaske; idan har akwai abu daya da ya tsaya kai da fata, to bai wuce soyayyar sa ga PDP ba; Na yi imani ba zai bar PDP ba.
“Yana wasa da tunanin mutane ne kawai, kuma hakan yana da kyau. Da Me zai amfana idan ya koma APC?” Momodu ya tambaya a cikin shirin Channels TV a yau Litinin.