Ma’aikata a Kasar Pakistan za su shafe tsawon kwanaki tara suna zallar hutun Sallah kamar yadda sanarwa ta fito.
Da ma dai adadin hutun da gwamnati ta ayyana zai kasance kwanaki shida ne daga ranar goma zuwa sha biyar ga watan Mayu, to sai dai ranakun 8 da 9 za su kasance ne a karshen makon, ranakun da tun asali na hutu ne.
Kazalika ranar 16 ga watan Mayu da ya kamata hutun kwanaki shidan ya kare zai sake kasancewa ne ranar Lahadi lamarin da zai sa dole Ma’aikata su shafe kwanaki takwas suna hutun Karamar Sallah.
Cikin wata sanarwa da Gwamnatin kasar ta fitar ta ce wa’adin kwanaki biyar da ta diba wa ma’aikatan ya biyo bayan shawara ce daga ɓangarori mabanbanta dake nuni da cewa ya kamata a bar ma’aikata su dan sararar ganin cewa lokacin zai kasance ne ba jina da kammala azumin watan Ramadan ba.
Da ma dai kasar Pakistan kasa ce wacce mafiya akasarin al’ummar ta Musulmai ne.