Mahaifin wata mambar NYSC da aka yi garkuwa da ita a jihar Zamfara, ya zargi hukumomin tsaro da hukumar masu yi wa kasa hidima ta kasa da nuna ko in kula kan lamarin.
Diyar Emmanuel Etteh na daya daga cikin dalibai takwas da aka yi garkuwa da su ‘yan Uyo, a jihar Akwa Ibom zuwa sansanin su na NYSC.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa Wasu ‘yan bindiga sun yi awon gaba da mambobin hukumar NYSC 8 a kan wata babbar hanya da ke jihar Zamfara a ranar Asabar, 19 ga watan Agusta.
Lamarin ya faru ne yayin da ‘yan NYSC din ke tafiya a cikin wata motar AKTC daga garin Uyo na jihar Akwa Ibom zuwa jihar Sokoto, akan hanyarsu ta jihar Zamfara domin shiga cikin aiki hidimar kasa na wajibi.
KARANTA WANNAN An Yi Garkuwa Da Mambobin NYSC A Jihar Zamfara
A cikin wani shiri kai tsaye a gidan Talabijin na Channels mai suna Sunrise Daily a ranar Litinin din nan, Etteh ya bayyana matsalar da ta shafe makonni biyu ana fama da ita a matsayin mummunar barna, ganin rashin ko in kula daga bangaren hukuma.
Ya ce, “Abin takaici ne matuka, domin a matsayina na Uba, gwamnati ta ji kunya matuka. Tun bayan faruwar wannan lamari babu wanda ya yi magana ko ya tambaya.
“Hukumomin tsaro ba su damu ba, shugabancin NYSC bai nuna damuwa ba, kuma kowa ya yi kamar ba abun da ya faru.
“Kowane aiki yana gudana, kuma ina ci gaba da tambaya, ‘Shin irin wannan gwamnati ce muke so wa kasarmu? Shin da irin wannan tsaro ne za mu iya samun kwanciyar hankali da shi?’ Hukumar NYSC ta gayyaci yaran daga gidajensu zuwa Sokoto.”
Jaridar PUNCH ta rawaito cewa Mahaifin wanda abin ya shafa ya bayyana rashin jin dadinsa da babban daraktan NYSC, inda ya bayyana cewa yana fatan samun babban matsayi daga hukumar. Mahaifin ya ce hukumar NYSC ba ta cika ka’idojin da ake sa rai ba.
Etteh ya kara da cewa babu wanda ya damu da tuntubar iyaye ko tattauna wa kan lamarin.
A Wani Labarin Kuma Tinubu Ya Jagoranci Taron Majalisar Tsaro Gabanin Tafiyarsa Indiya
Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu, a ranar Litinin din nan da rana, ya jagoranci taron kwamitin tsaro na kasa a fadar gwamnati da ke Abuja.
Duk da cewa ba a bayyana cikakken bayanin taron ba, jaridar PUNCH ta tattaro cewa an kira taron ne domin duba halin da ake ciki na tsaro da kuma shugabannin hafsoshin su yi wa shugaba Tinubu bayani kafin ya tashi zuwa birnin New Delhi na kasar Indiya.