Kamaru Usman, dan Najeriya, wanda ya sha kashi na farko a gasar UFC a filin wasa na Vivint Arena, dake birnin Salt Lake City, na kasarAmurka, a safiyar Lahadi, ya sha alwashin dawowa kan ganiyarsa.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito yadda Leon Edwards dan kasar Birtaniya ya doke Usman wajen lashe gasar Welterater UFC.
Usman ya farfado a farkon gasar a kokarinsa na kare kambunsa, yayin da yake hankoron zarce Anderson Silva wajen yawan lashe gasar na Welterater UFC.
KARANTA WANNAN LABARIN: Duk Cikin Yan Takarar Gwamnan Kano Babu Mai Kwarewata – Gawuna
Amma Edwads ya farfado daga bisa inda ya daki Usman aka wanda ya bashi nasarar lashe gasar da 4:04 a zagaye na 5.
Wanda ya ci gasar ya yi fariya inda bayan nasarar ya ke cewa, “Duk kun yi shakku da ni, kuna cewa ba zan iya ba – ku dube ni yanzu”
Amma da yake mayar da martani a cikin sakon da ya wallafa a shafinsa na twitter bayan ya yi rashin nasara, Usman ya ce, “Zakara yau ya gaza, Amma zan farfado a wani lokacin…”
Majiyar Jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito cewa, an haife Usman ne a garin Auchi na Jihar Edo dake Najeriya, a ranar 11 ga Mayun shekarar 1987, mahaifin Usman, wanda ya zama masanin harhada magunguna a Amurka, ya kawo iyalinsa cikin kasar lokacin Usman yana da shekaru takwas kacal da haihuwa a duniya.
A WANI LABARIN KUMA: Ba Zamu Sanar Da Sakamakon Zabe ta Intanet Ba – INEC
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa INEC ta ce za a gudanar da tattara sakamakon zaben shekarar 2023 da hannu ba tare da amfani da Intanet ba.
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa hakan zata faru ne duk kuwa da yadda aka tsara amfani da na’urar Kwamfuta waje tantance sakamakon zaben.
Kwamishinan INEC na kasa kuma shugaban kwamitin yada labarai da wayar da kan masu kada kuri’a, Festus Okoye, ya jaddada cewa hukumar za ta mika sakamakon zabe daga rumfunan zabe zuwa tasharta ta duba sakamakon zaben, , kamar yadda aka shaida a zabukan da suka gabata, amma dokar zabe ta fito karara kan yadda ya kamata a yi tattarawa.
Okoye ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da manema labarai s karshen mako, inda ya ce, “Akwai bambanci sosai tsakanin canja wuri/fitar da sakamakon da kuma tattara sakamakon.
Sashi na 50(2) na dokar zabe, ta 2022 ya baiwa hukumar ikon sanin yanayi da tsarin zabe a zabe da kuma yada sakamakon zabe.
“Sashe na 60 da 62 na dokar zabe ne ke tafiyar da tsarin bayan zabe da tattara sakamakon zabe.
Sashi na 60(1) na dokar ya tanadi cewa, bayan kidaya kuri’u a rumfar zabe, shugaban hukumar zai shigar da kuri’un da kowane dan takara ya samu a cikin fom da hukumar ta tsara.
“Sashe na 60 (5) na dokar ya zama wajibi shugaban hukumar ya mika sakamakon zaben, gami da adadin wadanda aka amince da su da kuma sakamakon kuri’un ta hanyar da hukumar ta tsara.
Bayan haka, shugaban hukumar bayan nadawa da sanar da sakamakon zai bayar da makamancin haka tare da kayayyakin zabe a karkashin kulawar jami’an tsaro tare da rakiyar ’yan takara ko wakilansu, inda za a samu wanda hukumar ta tsara.
“Ma’anar wannan ita ce har yanzu tsarin tattara sakamakon na hannu da hannu ne, amma jami’in tattara sakamakon dole ne ya tattara sakamakon bincikensa tare da tabbatar da cewa adadin wadanda aka amince da su da aka bayyana kan sakamakon da aka tattara daidai ne kuma sun yi daidai da adadin wadanda aka amince da su. rubutawa kuma ana watsa shi kai tsaye daga rumfunan jefa ƙuri’a.”
Ya bayyana cewa, yayin da za a gudanar da tattara sakamakon da hannu, inda aka samu sabani dangane da sakamakon da aka tattara ko kuma sakamakon wani sashe na zabe, jami’in tattara sakamakon zaben zai yi amfani da asalin sakamakon da aka yi ta cece-kuce, da bayanan tantancewa. daga na’urar BVAS da sakamakon da aka watsa kai tsaye daga sashin jefa kuri’a don tantance daidaiton sakamakon.